Communiqué de Presse
Pour diffusion immédiate le 5 Novembre 2021
L’Ambassade des États-Unis à Niamey déplore la mort des victimes et condamne les auteurs de l’attentat terroriste dans la région de Tillaberi
L’ Ambassade des États-Unis à Niamey et le peuple américain expriment leurs condoléances les plus sincères aux familles des victimes de l’attaque terroriste perpétré le 4 novembre contre des personnes innocentes à Banibangou dans la région de Tillabery. Nous nous joignons au people du Niger dans ce deuil national.
Les États-Unis condamnent fermement ces attaques impies des terroristes, qui ne servent aucune cause. Il n’y a pas de place dans le monde moderne pour des attaques lâches contre des innocents civils.
Pendant que nous cherchons à éradiquer la région de l’extrémisme violent et son idéologie impie, nous réitérons notre engagement et notre partenariat avec le peuple nigérien et les Forces Armées Nigériennes.
———————————————————————————————————————————————————-
Ofishin Jakadancin Amurka a Yamai
Sanarwar manema labarai
Nuwamba 5, 2021
Ofishin Jakadancin Amurka a Yamai ya yi Allah wadai da mutuwar wadanda aka kashe tare da yin Allah wadai da wadanda suka kai harin ta’addanci a yankin Tillaberi.
Ofishin jakadancin Amurka a Yamai da al’ummar Amurka sun mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ta’addancin da aka kai a birnin Banibangou na yankin Tillabery a ranar 4 ga watan Nuwamba. Muna tare da al’ummar Nijar a wannan makoki na kasa baki daya.
Amurka ta yi kakkausar suka kan wadannan hare-haren da ‘yan ta’adda suka kai na rashin tsoron Allah, wadanda ba su da wata manufa. A wannan zamani babu inda ake kai hare-hare na matsorata a kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
A yayin da muke kokarin kawar da ta’addanci da akidarsa na rashin tsoron Allah na wannan yanki, muna kara jaddada kudurinmu da hadin gwiwa da al’ummar Nijar da sojojin Nijar.