L’ambassade des États-Unis condamne fermement les récentes attaques terroristes au Niger

le 4 Janvier 2021

Au nom du peuple américain, l’ambassade des États-Unis présente ses plus sincères condoléances aux membres de familles des victimes des récentes attaques terroristes de Tchombangou, Zaroumadarèye, et Toumour.

Les États-Unis condamnent de la manière la plus forte ces attaques terroristes et toutes les autres formes de violence.  Ces attaques lâches et abominables doivent cesser. Il n’y a pas de place dans le monde moderne pour la violence contre des innocents.

Nous restons attachés aux forces armées du Niger et à nos alliés dans l’éradication de ces extrémistes violents et de leur idéologie impie.

 

Sanarwa, Ranar 4, janairu 2021

Ofishin Jekadancin Amurka a Niger ya yi Allah wadai da Hare-Haren ta’addanci na baya bayan nan a kasar Niger

Da sunan al’umar kasar Amurka, ofishin jekadancin Amurka a Niger na meka ta’aziya ga iyallan mutanenda hare haren ta’addanci da suka wakana baya bayan nan suka rutsa da su a garuruwan Tchombangou, Zaroumadarèye, da Toumour.

Gwamnatin Amurka ta yi Alla wadai da kakausar murya a game da hare-haren  yan ta’adda da duka wani salo na nuna karfi ko mugunta.  Dole ne a takawa wadannan munanan hare- hare da wasu marasa imani ke kaiwa birki.  Babu wurin zama ga ga ayyukan nuna karfi fiye da kima ko mugunta ga bayin Allah da basu ji ba su gani ba, a wannan zamani.

Muna kara jaddada kawo goyon bayan mu ga rundunar sojojin Niger, da kawayen mu a cikin yaki da ayyukan ta’addanci domin kawarda masu matsannanciyar aqida kuma marasa imani.