L’Ambassade des États-Unis honore huit journalistes nigériens à l’occasion de la Journée Mondiale de la Liberté de Presse.

Ambassade des Etats-Unis d’Amérique, Niger

 

 

Communiqué de Presse

Pour diffusion immédiate le 04 mai 2021

Titre: L’Ambassade des États-Unis honore huit journalistes nigériens à l’occasion de la Journée Mondiale de la Liberté de Presse.

L’Ambassade des États-Unis à Niamey a honoré huit journalistes nigériens lors d’un Iftar à la résidence de l’Ambassadeur Whitaker, le 3 mai 2021. L’évènement, organisé à l’occasion de la Journée Mondiale de la Liberté de Presse, a célébré les journalistes nigériens et leur rôle vital au Niger. Elle a également marqué l’achèvement du Programme « Professionnalisation des journalistes nigériens pour une couverture électorale » de l’Ambassade. L’Ambassade s’est associée à l’Association des Professionnelles Africaines de la Communication (APAC-Niger) pour diriger le programme.

En plus des prix pour les huit lauréats, le programme a offert une formation à trois journalistes sélectionnés dans chacune des huit régions du Niger afin de couvrir les élections au Niger, la transition post-électorale et le début de l’administration actuelle. Le programme a également parrainé un concours national de journalisme « Meilleures Œuvres Journalistiques pour des Elections Pacifiques au Niger ». Les journalistes ont pu soumettre leurs travaux sur des élections pacifiques dans quatre catégories : radio, télévision, presse écrite et en ligne.

L’Ambassade des États-Unis et APAC-Niger ont déclaré les lauréats lors d’une cérémonie de remise de prix pendant l’Iftar. Le jury, composé de membres du personnel de l’Ambassade des États-Unis, de l’APAC-Niger, de la Maison de la Presse et des médias indépendants, a évalué et noté des dizaines de travaux avant de sélectionner les gagnants.

Les résultats sont donc les suivants :

Radio 1er Prix :  Sakinatou Abdou Sanda, Radio et Télévision Niger 24

Radio 2ème Prix :  Maman Sani Abdou Haladou, Radio Anfani, Maradi

 

Télévision 1er Prix :  Algalass Addine, ORTN, Tillabery

Télévision 2ème Prix :  Moumouni Moussa Ismael, Télévision Labari

 

Presse Ecrite 1er Prix :  Ali Maman, ONEP

Presse Ecrite 2ème Prix :  Mahaman Moustapha Omar, La Nation

 

Presse En Ligne 1er place :  Maman Sabo Bachir, Agence Nigérienne de Presse

Presse En Ligne 2ème Prix :  Abdou Tsahirou, Agence Nigérienne de Presse, Tahoua

 

Au cours de la cérémonie de remise des prix, l’Ambassadeur Whitaker a souligné le fort engagement des États-Unis envers la liberté de presse au Niger : « Une presse libre et transparente facilite l’échange d’informations vitales, le combat contre la corruption et la défense des droits humains. Nous continuerons d’offrir des programmes de formation et d’échanges pour les journalistes aux États-Unis. Nous ne cesserons d’appuyer les journalistes notamment dans leurs efforts pour assurer une presse libre et impartiale au Niger, qui renforce la démocratie, la liberté d’expression et les libertés civiles. Nous demeurons un partenaire dans cet effort vital. »

——————————————————————————————————————————————————————————————————————————————————————————————————

Sanarwar Ofishin Jekadancin Amurka a Niger 

 

 

4 ga watan Mayu 2021

Kan Labari : Ofishin Jekadancin Amurka ta Karrama Yan JaridaTakwas (8) a Ranar Bikin Yancin Jarida ta Duniya

 

Ofishin jekadancin Amurka a Niamey ya karrama wasu yan jarida takwas (8) yayin wani taron buda-baki a gidan jekadan Amurka din Malam Eric P. Whitaker a ranar 3 ga watan Mayun 2021. 

Bikin da ya gudana a ranar bikin Yancin Yan Jarida Ta Duniya, ya girmama yan jaridar Niger din ne domin muhimmiyar rawarda suke takawa a Niger.  Bugu da kari, bikin ya kawo karshen wani zango na wani shiri na Ofishin Jekadancin Amurka mai manufar “Inganta Aikin Yan Jaridar Niger ta hanyar bin diddigin ayyukan zabe.”  Ofishin Jekadancin Amurka ya gudanarda wannan shiri ne tare da ban hannun Kungiyar Mata Kwarraru ta fannin aikin Jarida da Sadaswa (APAC-Niger).

Ko ba’ada bayarda tukwuici ga yan jaridar da suka yi nasara su takwas, Shirin ya bada horo ga wasu yan jaridar su ashirin da hudu, wato yan jarida uku da ga kowace jaha gabanin zabe, yayin zabe da kuma bayan zabe zuwa hawan sabuwar gwamnati a kan karagar Mulki.

Har ila yau, Shirin ya tanadi tukwuici ga yan jaridar a fadin kasar a cikin wata gasa mai taken “kyakkyawan Sakamakon aikin yan jarida a game da shirya zabe a cikin kwanciyar hankali a Niger.”

Yan jaridar sun yi nasar shiga wannan takarara a cikin rukunnan Rediyo, Talbijin, Jarida, da Yanar gizo.”

Ofishin Jekadancin Amurka da kungiyar APAC-Niger sun bada tukwuicin gasar yan jarida yayin wani taron alfarma na  shan ruwa (Iftar).  Alkalan gasar sun fito daga Ofishin jekadancin Amurka, Apac-Niger da uwar kungiyar yan jaridar Niger (Maison de la Presse), har ma da wasu kafofin yada labarai masu zaman kansu. Kuma sun yi aiki ne a kan gwamman yan takara.

Ga sakamakon gasar kamar haka:

Rediyo Lamba 1: Sakinatou Abdou Sanda, Rediyo & Talbijin Niger 24

Rediyo Lamba 2:  Maman Sani Abdou Haladou, Rediyo Anfani, Maradi

Talbijin lamba 1: Algalass Addine, ORTN, Tillabery

Talbijin lamba 2:  Moumoni Moussa Ismael, Gidan Talbijin Labari

Jarida Lamba 1 :  Ali Maman, Madaba’a ONEP

Jarida lamba 2 :  Mahaman Moustapha Omar, Jaridar La Nation

Jaridar Yanar Gizo 1 :  Maman Sabo Bachir, Madaba’ar Agence Nigérienne de Presse (ANP).

Jaridar Yanar Giza lamba 2 :  Abdou Tsahirou, Agence Nigérienne de Presse, Tahoua

A yayinn bikin karrama yan jaridar, Jekadan Amurka a Niger Eric P.Whitaker ya jaddada himmantuwar Amurka a game da kare hakkin yan jarida. Shi na mai cewa « Kafafen yada labarai masu yancin fadar albarkacin bakinsu na masu saukaka hulda da musanyar bayannai da ka iya taimakawa ga kare lafiyar al’ummomi, yaki da rashuwa, da kare hakin bil’adama. Zamu ci gaba da taimakawa yan jarida a cikin kokarinsu na tabbatarda kafofin yada labarai masu yanci da kwatanta adalci a kasar Niger wanda hakan ke bunkasa Dimokradiya, yancin fadar albarkacin baki, da yancin bil’adama. Zamu kasance cikkakun abokan hulda a cikin wannan  muhimmin yunkuri. »

 

####