Un otage américain retrouvé au Niger

Ambassade des Etats-Unis d’Amérique, Niger

 

Communiqué de Presse

Un otage américain retrouvé au Niger

 

Les États-Unis se félicitent la libération d’otage américain, Jeffery Woodke, qui était enlevé au Niger en 2016.  Nous exprimons notre profonde gratitude et notre appréciation à nos partenaires nigériens et des autres pays qui ont aidé à obtenir la libération de l’otage.  Des responsables américaines sont en contact avec lui, et lui apporte toute l’aide appropriée.

L’administration Biden n’a pas de plus grande priorité que de ramener à la maison les ressortissants américains retenus en otage ou détenus à tort, et nous continuerons à travailler inlassablement pour assurer leur liberté dans le monde entier.

Le 20 mars, le Secrétaire d’État Antony J. Blinken a publié la déclaration suivante :

Nous nous réjouissons de la libération du citoyen américain Jeffery Woodke, retenu en otage en Afrique de l’Ouest pendant plus de six ans. J’ai parlé avec la famille de Jeffery aujourd’hui et je suis heureux qu’il soit bientôt réuni avec elle. Nous sommes reconnaissants au gouvernement du Niger pour sa coopération extraordinaire, ainsi qu’à d’innombrables organisations et personnes dans le monde entier dont les efforts ont abouti à la libération de M. Woodke. Je n’ai pas de priorité plus élevée que de ramener chez eux des ressortissants américains retenus en otage ou détenus arbitrairement à l’étranger, et nous continuerons à travailler sans relâche pour leur liberté dans le monde entier.


Ofishin Jekadancin Amurka a Niger

 

Sanarwar Manema Labarai

Don fitowa nan take Maris 21, 2023

An yi garkuwa da wani Ba’amerike a Nijar

Amurka ta yi maraba da sako ba’amerike da aka yi garkuwa da shi, Jeffery Woodke, wanda aka yi garkuwa da shi a Nijar a shekarar 2016. Muna nuna matuƙar godiya da yabon  abokan huldarmu a Nijar da sauran kasashen da suka taimaka wajen ganin an sako mutanen. Jami’an Amurka suna tuntubar sa, kuma suna ba shi duk taimakon da ya dace.

Gwamnatin Biden ba ta da fifiko fiye da dawo da ‘yan Amurka da aka yi garkuwa da su ko kuma a tsare su ba bisa ka’ida ba, kuma za mu ci gaba da yin aiki tuƙuru don tabbatar da ‘ƴancinsu a duniya.

A ranar 20 ga Maris, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony J. Blinken ya ba da sanarwar mai zuwa:

Muna maraba da sakin dan kasar Amurka Jeffery Woodke, wanda aka yi garkuwa da shi a yammacin Afirka sama da shekaru shida. Na yi magana da dangin Jeffery a yau kuma na yi farin ciki da za ya sake saduwa da su nan ba da jimawa ba. Muna godiya ga gagarumin hadin kan da gwamnatin Nijar ta ba mu, da kuma ci gaba da kokarin kungiyoyi da daidai kun mutane a fadin duniya da suka yi sanadin sakin Mista Woodke. Ba ni da fifiko fiye da dawo da ƴan ƙasar Amurka da aka yi garkuwa da su ko kuma aka tsare su ba bisa ƙa’ida ba a ƙasashen waje, kuma za mu ci gaba da yin aiki tuƙuru don tabbatar da ‘ƴancinsu a duniya.